- Addinin Musulunci na cigaba da fuskantar kalubale a wasu kasashen duniya musamman a wasu yankunan Amurka
- Wata tsohuwar ‘yar takarar a jam’iyyar Republican, Valentina Gomez, ta tayar da hargitsi a taron Musulmi a Capitol na Texas
- Mutane da dama sun yi korafi tare da sukar matakin da yar siyasar ta ɗauka yayin taron da aka yi a kudancin Amurka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Texas, US – Tsohuwar ‘yar takara a jam’iyyar Republican ta jawo maganganu bayan kutsawa cikin taron Musulmi a kasar Amurka.
Valentina Gomez, ta hargitsa wani taron al’ummar Musulmi a Capitol na Texas, inda ta kwace makirufo tare da yin kalaman batanci.
Asali: Twitter
Rahoton Aljazeera ya wallafa wani bidiyo da ke nuna abin takaicin da yar siyasar ta aikata a Texas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Gomez ke yi ga Musulunci
Daman Gomez ta saba wallafa bidiyo inda take yin barazana ga al’ummar Musulmi da kuma kalaman batanci ga addininsu.
Ta taba yin rubutu da kuma wallafa bidiyo inda take cewa idan ta samu damar zuwa majalisa za ta hana yaɗuwar Musulunci.
An gano ta bidiyon tana kona Alkur’ani yayin da take kalamai marasa daɗi ga addinin Musulunci.
Daga baya, Gomez ta wallafa faifan bidiyon a X tana cewa:
“Musulunci ba shi da wuri a birnin Texas, Ubangiji kadai na ke tsoro.”
Asali: Twitter
Yar siyasa ta tarwatsa taron Musulmi a Amurka
Wannan lamari ya faru ne yayin wani taron wayar da kai na Musulmai, bidiyon da aka yada sun nuna Gomez tana cin zarafin Musulunci a fili.
Taron ya kasance bangare na ‘Texas Muslim Capitol Day’, da aka shirya taro, addu’a, horaswa, cin abinci, da ganawa da jami’an gwamnati.
Kungiyar CAIR da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙi sun la’anci halayyar Gomez, suna mai neman a ɗauki mataki tare da kare ‘yancin yin addini.
Kara karanta wannan
JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi
Ce-ce-ku-ce da Gomez ke jawowa a kafofin sadarwa
Ba wannan ne karo na farko Gomez ta jawo cece-kuce ba, a Disambar 2024, ta saki bidiyon wasu bidiyo da ke sukar yan luwadi.
Hakan ya sa kafofin sada zumunta suka takaita bidiyon saboda keta ƙa’idar hana tashin hankali.
A Fabrairu, ta kuma ƙone littattafan LGBTQ+ a bainar jama’a, tana cewa za ta hana irin su idan aka zaɓe ta, tana sukar yan Daudu.
An haifi Valentina Gomez a Medellín, Colombia, a 1999, daga bisani suka koma Amurka a 2009, inda suka zauna a birnin Jersey.
Ta fara shahara ne a harkar saka jari na gidaje kafin ta shiga siyasa, a Missouri, ta yi takarar sakataren jiha amma ta sha kaye.
An soki Minista kan take hakkin Musulmi
Kun ji cewa ministar tsaron jama’a na Finland, Sanni Grahn-Laasonen ta jawo ce-ce-ku-ce kan kalamanta game da sanya hijabi a makaranta.
Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: Fitacciyar ‘yar wasan barkwanci ta rasu a ‘taron matar gwamna’ a Najeriya
Minstar ta ce hijabi bai dace da makarantu ba a kasar, lamarin ya jawo suka daga Musulmi da aka sani da yawan lullube jikinsu.
Sakatariya a kungiyar Musulmi, Pia Jardi ta ce babu ‘yan ta’adda a Finland, ta gargadi cewa tattaunawar na iya kaiwa har a hana hijabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng